Thursday, July 16
Shadow

Duk da saukar farashin mai a kasuwannin Duniya, ‘Yan kasuwar man fetur na Najeriya sun ki rage farashi

Rahotanni na cewa a kasuwar Duniya, Farashin danyen man fetur ya fadi zuwa dala $100 daga dala $130.

Saidai duk da hakan, ‘yan kasuwar man fetur din na Najeriya suna ci gaba da sayar da man da tsada a farashin Naira 1,300 akan kowace lita.

Saukar farashin a kasuwar Duniya ya farune a yayin da ake tsammanin tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Iran zata haifar da da me ido.

Saidai duk da wannan, gidajen man fetur a Najeriya ciki hadda na gwamnati, NNPCL suna sayar da man akan farashi sama da Naira 1,300 a wasu gidajen man ma har sama da hakan.

Hauhawar farashin man fetur din a Najeriya yasa an samu hauhawar wasu kayan masarufi dama ababen hawa.

Karanta Wannan  Kungiyar Manyan ma'aikatan Man fetur, PENGASSAN ta baiwa membobinta umarnin dakatar da aikawa matatar Man Fetur ta Dangote Danyen Mai da Gas, Dangoten ya koka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *