
Masu garkuwa da mutane a ranar 24 ga watan Disamba daya gabata na shekarar 2024 sun yi garkuwa da dan siyasa na jihar Anambra me suna Hon Justice Azuka.
Sun yi garkuwar dashine a garin Onitsha bayan nuna masa bakin Bindiga.

‘Yansanda sun yi nasarar kama wadanda ake zargi da wannan aika-aika inda suka amsa laifinsu.
A ranar 6 ga watan Fabrairu na shekarar 2025 ne wanda ake zargin suka kai ‘yansanda gadar Second Niger Bridge inda suka ce anan ne bayan sun kashe Hon Justice Azuka suka jefar da gawarsa.
Hadin gwiwar jami’an tsaro yayi nasarar gano gawar dan siyasar wadda har ta fara rubewa.
Justice Azuka dan Jam’iyyar Labour party ne kuma yayi nasarar kwace kujerar majalisar tarayya ne daga hannun dan takarar Jam’iyyar PDP Hon. Douglas Egbuna a kotu shekara daya kamin faruwar wannan lamari.