Saturday, March 15
Shadow

Amurkawa na zuwa Asibitocin Najeriya neman magani>>Inji Gwammatin Tarayya

Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa, an samu ci gaba sosai a Najeriya musamman ta fannin lafiya inda yace ‘yan kasar Amurka na zuwa Najeriya neman magani.

Ya bayyana hakane a yayin ganawa da wata kungiyar Likitocin da suka kai masa ziyara a Abuja fadar shugaban kasa.

Yace kwanannan wasu marasa lafiya daga kasar Amurka su 13 suka zo Asibitin Zenith Medical and Kidney Centre aka musu dashen koda kuma an samu nasarar yin aikin.

Yace kuma sun samu aikin a farashi me sauki kasa da yanda ake yinsa a kasar ta Amurka.

Mataimakin shugaban kasar ya kuma jinjinawa shugaban Asibitin me suna Dr. Olalekan Olatise inda yace gwarzo ne wajan kula da lafiya.

Karanta Wannan  Rahotanni sun ce, Israela ta kashe Falasdinawa 50 a wani mummunan hari data kai Rafah, Kalli Bidiyon yanda mutane suka kone kurmus

Saidai ya koka game da yanda ‘yan Najeriya da yawa ke fama wajan aikin Koda saboda tsadarsa inda yace wasu na dogaro da gwamnati ta dauki nauyin aikin inda wasu saidai su sayar da gida dan biyan kudin aikin saboda tsadarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *