
Rahotanni sun bayyana cewa, kamfanin wutar lantarkin dake kula da wutar lantarki ta Kaduna, Zamfara, Kebbi da Sokoto dake yajin aiki sun janye yajin aikin nasu da ya kwashe kwanaki biyar suna yi.
Ma’aikatan kamfanin wutar sun janye yajin aikinne bayan da gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya shiga tsakani.
Gwamnan ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda ya tabbatar da cewa, an janye yajin aikin.