
Tsohuwar Ministar Harkokin Mata, Uju Kennedy-Ohanenye, ta dawo masana’antar Nollywood tare da sabon fim dinta mai suna “Hatred”.
Fim ɗin, wanda ita ce ta shirya, ya kasance alamar dawowarta a hukumance cikin masana’antar bayan tsawon lokacin da ta yi a harkar siyasa.
An naɗa Kennedy-Ohanenye a matsayin ministan Shugaba Bola Tinubu a ranar 21 ga Agusta, 2023, amma aka tsige ta daga mukaminta a ranar 23 ga Oktoba, 2024, tare da wasu ministoci hudu.
VANGUARD ta rawaito tun bayan barin ta ofis, matar mai shekaru 51 ta koma mayar da hankali kan harkar shirya fina-finai da fasaha.