
Tsohon Kwamishinan zabe na jihar Adamawa, Barr Hudu Ari ya bayyana cewa bai damu ba dan an koreshi daga aiki ba saboda shi yasan cewa, A’isha Dahiru Binani ce ta lashe zaben Gwamnan jihar Adamawa.
Hakan na zuwane kasa da mako daya bayan da majalisar tarayya ta amince da korarsa daga aiki.
Tuni dai dama aka dakatar dashi saboda bayyana cewa Binani ce taci zabe a yayin da ake kan tattara sakamakon zaben.
Saidai har yanzu, Ari ya bayyana cewa yana da takardu da hujjoji dake tabbatar da cewa A’isha Binani ce ta lashe zaben gwamnan jihar Adamawa, ba Gwamna me ci Ahmad Fintiri ba.
Ya bayyana hakane a yayin ganawa da manema labarai a gidansa dake Bauchi inda har sai da ya rantse da Qur’ani.
Yace an matsa masa sai ya bayyana gwamna Ahmad Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben kuma har Farfesa Yakubu ya gabatarwa da hujjojinsa na cewa Binani ce ta lashe zaben amma yaki sauraronsa.