
Tauraron TikTok, G-Fresh Al-amin ya mayar da martani kan masu cewa, shima ‘yan uwansa su taru su dakeshi kamar yanda akawa Yahya Y America.
G-Fresh yace shi ‘yan uwansa ba ‘yan gargajiya bane kuma ahi ba bata tarbiyya yake ba, Gyaran Tarbiyya yake.
Yace kuma ya hada aure kusan 4 kuma babu wanda ya biyashi, Allah ne ya biyashi.
Yace a lokacin da suke gwagwarmaya babu wanda ya damu dasu sai da suka samu daukaka ne ake neman a rika saka baki a rayuwarsu.