Hukumar Hisbah Ta Jihar Kano Ƙarkashin Jagorancin Shéikh Malam Aminu Ibrahim Daurawa Ta Kama Mawaƙin Kuma Jarumin TikTok Al’amin G-Fresh
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke mawakin nan kuma Jarumin TikTok Al’amin G-Fresh.
Bayanan da Freedom Radio ta samu sun nuna cewa Hisbah ta kama G-Fresh saboda zargin yiwa Alkur’ani Mai Girma Izgili da kuma yin kalaman batsa.
Karin bayani:
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta kama fitaccen mai amfani da shafukan sada zumuntar nan da aka fi sani da G-Fresh
Babban daraktan hukumar Mallam Abba Sufi ne ya tabbatar wa BBC labarin kama matashin.
Ya ce hukumar ta kama shi bayan jerin gargaɗin da ta yi masa sakamakon abubuwan da yake wallafawa a shafukan sada zumunta.
”Mun kama shi ne bayan tarin gargadin da muka sha yi masa kan abubuwan na baɗala da rashin kunya da yake wallafawa shafukansa na sada zumunta”, in ji Abba Sufi.
[…] A baya dai, mun ji rahoton yanda Hukumar Hizbah dake Kano ta Kama G-Fresh Al’amin bisa zarge-zarge. […]