Tauraron mawaki kuma dan Tiktok, G-Fresh Al’amin ya bayyana cewa, ya tuba ya daina maganganin batsa.
Ya bayyana hakane a shafinsa inda yace manya sun masa maganar rashin dacewar hakan.
Saidai yace ba zai daina yaki da kamfanin dan malele ba.
Ya kuma bayyana cewa Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya sakashi a Islamiya, zai rika zuwa daukar darasi.
A baya dai, mun ji rahoton yanda Hukumar Hizbah dake Kano ta Kama G-Fresh Al’amin bisa zarge-zarge.