
Wata baturiya a kasar Amurka ta kai Asibiti kotu saboda kuskure wajan zuba mata maniyyi da aka yi.
Matar me suna Krystena Murray ‘yar kimanin shekaru 38 ta zabi namiji me kama da itane farar fata inda tace a saka mata maniyyinsa.
Saidai an samu kuskure aka saka mata maniyyin namiji bakar fata kuma ta haifi jariri bakar fata, saidai duk da haka ta kudiri aniyar ci gaba da renon jariri.
Saidai daga baya masu maniyyin ashe suma sun ajiyene dan amfani dashi nan gaba, inda suka kaita kara wanda a dole ba tana so ba ta basu jaririnsu.
Saidai itama yanzu ta kai Asibitin me suna Coastal Fertility Specialists kara inda take neman a bi mata hakkinta kan wannan kuskure da suka tafka akanta.
Ta shigar da karar ne a Kotun, Chatham County dake Georgia.
Ta bayyana cewa, babban burinta a rayuwa shine ta zama uwa.