
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, ya kamata a jinjinawa tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar kan kokarin gyaran tattalin arzikin da yayi a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.
Ya bayyana hakane a wajan gaisuwar marigayi, Edwin Clark a jihar Delta.
El-Rufai yace yawanci mutane sun fi tunawa da abin ashsha da mutum ya aikata fiye da abin alkairi.
El-Rufai yace hadda shi sun yi aiki a karkashin Atiku suka gyara tattalin arzikin kasarnan a lokacin amma ba’a magana akan lamarin ko dan basu yi rubutu akan lamarin bane?