
Hukumar Kididdiga ta kasa, NBS ta bayyana cewa, farashin lemun kwalba, dana giya, dana taba dana sauran kwayoyi ne yafi kowane tashi a cikin kayan da ake amfani dasu a Najeriya.
Farashin wadannan kayayyaki kamar yanda NBS ta bayyana ya tashi da kaso 14.80 a cikin watan Janairu da ya gabata.
NBS tace kayan da suka fi tsada na biyu shine farashin kudin haya da na cin abinci a gidajen cin abinci a fadin kasarnan wanda ya tashi da kaso 14.14.
Abinda ke biye musu shine farashin kayan sawa, da tafiye-Tafiye, da takalma, wanda suma suka yi tashi sama.