
Tsohon Hadimin Shugaban kasa, Bashir Ahmad ya bayyana cewa, da Tsohuwar ministar kudi, Ngozi Okonjo Iwaela zata tsaya takarar shugaban kasa, zai zabeta.
Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda yace sauran wadanda zai zaba daga kasar Inyamurai idan sun tsaya takarar shugaban kasa sun hada da Chris Ngige, Dave Umahi, Ifeanyi Ugwuanyi, Geoffrey Onyeama, da Madam Sharon Ikeazor.
Saidai ya sha martani a wajan Inyamurai da yawa inda suka kalubalanceshi da cewa me yasa bai saka Peter Obi ba?