
Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya mayarwa da tsohon Hadimin shugaban kasa, Reno Omokri martani kan sukar da ya masa.
Omokri bayan da El-Rufai yace Shugaba Tinubu ne yaki bashi mukamin minista ba majalisa ce taki tantanceshi ba, ya cewa El-Rufai yan da hannu a kisan Kiristoci a kudancin kaduna, da kisan ‘yan Shi’a a Zaria, sannan ya zargi El-Rufai da yin barazanar kashe Turawa a kuma zagin Annabi Isa(AS).
Saidai a martanin El-Rufai ga Reno Omokri ta shafin X, yace Reno bashi da kunya.
Sannan yace Gwamnatin Tinubu ce ta daukeshi aikin kareta wanda abinda ake bukata wajan yin wannan aiki sun hada da rashin da’a, da rashin Tarbiyya da son yin kudi dare daya.