
Tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB ya bayyana cewa rashin cika alkawari da tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon yayi na kare rayuwar Inyamurai yasa aka fada yakin basasa.
Ya bayyana hakanne a cikin littafinsa daya rubuta me suna ‘Journey in Service’ inda ya kara da cewa, an rika yiwa Inyamurai kisan kiyashi a Arewa duk da alkawarin da Yakubu Gowon yayi na kare rayuwarsu.
Yace wannan ne yasa Ojukwu a wancan lokacin yace yace bai yadda ba ana cutar jama’arsa.
Yace Tun farko dai Da aka yi juyin mulki Yakubu Gowon ya zama shugaban kasa, Ojukwu yace bai yadda da Yakubu Gowon ya zama shugaban kasa ba saidai Brig Babafemi Ogundipe wanda a wancan lokacin shine soja mafi girman mukami.
Saidai Yakubu Gowon yayi ta kokarin ganin ya hada kan sa inda ya kira taron hadin kan kasa.
Lamura sun rincabe inda Ojukwu ya daina halartar taron majalisar Shugaban kasa.
Anan ne sai tsohon Shugaban kasar Ghana Lt-General Joseph Arthur Ankrah ya shiga tsakani inda aka je Aburi aka yi yarjejeniya tsakanin Gwamnatin Yakubu Gowon da Ojukwu wanda shine aka sawa yarjejeniyar sunan Aburi Accord.
Da aka dawo Najeriya, Shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon ya yi wata sabuwar doka me sunan Decree 8 inda ya nemi kowane bangare ya zo a saka mata hannu.
Saidai Ojukwu yaki amincewa da wannan doka inda yace ta sabawa yarjejeniyar Aburi Accord. Daga nan ne sai aka fada yakin basasa.