
Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi ta bayar da labarin yanda Kakakin majalisar Dattijai, Godswill Akpabio ya taba rike hannunta a gaban mijinta.
Tace a lokacin sun je taya Akpabio murnar zagayowar ranar haihuwarsa ne inda mijinta ya rakata.
Tace Sanata Akpabio ya kama hannunta ya jata ya rika nuna mata gidansa yayin da mijinta ke binsu a baya.
Tace abin ya damu mijinta a lokacin wanda daga nan ya rika cewa ba zata rika yin tafiya ita kadai ba.