
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin ƙasar na 2025 da ya kama naira tiriliyan 54.99
Kasafin kuɗin na wannan shekara ya zarta na shekarar da ta gabata – wanda aka yi a kan naira tiriliyan 27.5 – da kashi 99.96 cikin 100.
Shugaban ya sanya hannu kan kasafin ranar Juma’a a fadarsa da ke Abuja.
An dai ƙara yawan kasafin na farko da shugaan ya aikewa majalisa na naira tiriliyan 49.7.
A ranar 13 ga watan Fabrairun da muke ciki ne majalisar dokokin ƙasar ta amince da kasafin, bayan muhawara a kansa.
An dai tsara kashe naira tiriliyan 14.32 wajen biyan bashi, inda manyan ayyuka za su laƙume naira tiriliyan 23.96.