
Jam’iyyar APC a jihar Kebbi ta dakatar da Kabir Sani-Giant saboda kai maciji cikin gidan Gwamnatin jihar ya tsorata mutane.
Sakataren Jam’iyyar na jihar, Alhaji Sa’idu Muhammad-Kimba ne ya fitar da wannan sanarwa a ranar Lahadi.
Yace ranar February 8, 2025 Kabir ya shiga da maciji cikin gidan gwamnatin jihar inda ya tsorata mutane, yace hakan ya sabawa kundin tsarin Jam’iyyar.
Yace dakatarwar da akawa kabir zata ci gaba da zama har zuwa lokacin da za’a kammala buncike akansa.