
Matar marigayi tsohon gwamnan jihar Ondo, Betty Akeredolu ta bayyana cewa bai kamata kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya saka matarsa a cikin fadan da suke da Sanata Natasha Akpoti ba.
Tace kamata yayi ace ya tsaya an yi fadan dashi ba ya koma gefe ya turo matarsa ba.
Betty ta bayyana hakanne a kafar X.
Tace kuma Sanata Natasha Akpoti ta birgeta data fito ta nuna rashin jin dadinta kan canja mata kujera ba tare da saninta ba.
Tace dan an yiwa wasu sun yi shiru hakan ba yana nufin itama ta yi shiru bane.
tace irin su Sanata Natasha Akpoti ne ya kamata ace mata suna sakawa a gaba dan su jagorancesu musamman a majalisa.