Gwamnatin tarayya ta jaddadawa Kungiyar Kwadago cewa, ba zata iya biyan Sama da Naira Dubu 60 ba a matsayin mafi karancin Albashi ba.
Hakan na zuwane a Yau, Litinin da kungiyar ta kwadago ta fara yajin aikin sai baba ta gani.
Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi ya bayyanawa kungiyar kwadagon da ma’aikatan gwamnatin tarayya cewa tafiya zuwa yajin aiki sabawa doka ne.
Yace kuma zasu iya fuskantar daurin watanni 6 saboda tafiya yajin aikin.
Ya bayyana cewa, har yanzu akwai tattaunawa tsakanin gwamnati da kungiyar kwadagon kuma ba’a kammala ba dan haka bai kamata kungiyar ta tafi yajin aiki ba.
Ya roki kungiyar kwadagon data sake tunani kan wannan mataki data dauka inda yace bai kamata ba dan zai jefa da yawan ‘yan Najeriya cikin halin kaka nikayi da wahala.