
Babbar kotun tarayya dake Abuja ta dakatar da yunkurin ladaftar da Sanata Natasha Akpoti da majalisar tarayya ke shirin yi.
Lauyoyin Sanata Natasha Akpoti ne suka shigar da kara inda suke neman kotun ta dakatar da kwamitin ladaftarwa dake neman tuhumar sanata Natasha Akpoti.
Mai Shari’a Justice Obiora Egwuatu ya amince da wannan bukata inda yace an dakatar da wannan bincike.
Yanzi dai majalisar ba zata iya ci gaba da binciken sana Natasha Akpoti ba har sai idan an samu daukaka kara ko wani sabon hukuncin ya fito.