Friday, December 5
Shadow

Najeriya ta zo ta shida a cikin kasashen da aka fi aikata ayyukan tà’àdàncì a Duniya na shekarar 2025

Najeriya ce ta zo matsayi na 6 a cikin kasashen da aka fi aikata ayyukan ta’addanci a Duniya a shekarar 2025.

A shekarun 2023 da 2024 Najeriya tana matsayi na 8 ne.

Kasar Burkina Faso ce ta zo a matsayi na farko sai kuma kasar Pakistan na biye mata baya inda kasar Syria ta zo ta 3.

Mali ce ta 4 sai kasar Nijar ta 5 sai Najeriya ta zo ta 6.

Hakanan rahoton yace an samu yawan mutanen da aka kashe ta sanadiyyar ta’addanci a Najeriya wanda yawansu ya kai mutane 565 jimulla.

Karanta Wannan  ''Yan Bìndìgà sun kashe daliba Maryam da suka sace a jami'ar jihar Zamfara duk da karbar kudin Fansa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *