
Majalisar tarayya ta amince da kudirin dokar toshe duk wani shafin yanar gizo dake nuna Bidiyo da hotunan tsiraici wanda aka fi sani da Blù fìm.
Majalisar tace hukumar sadarwa ta kasa,NCC ta baiwa duka kamfanonin dake samar da Internet a Najeriya umarnin toshe shafukan dake nuna batsa nan take.
Dan majalisa daga jihar Katsina, Dalhatu Tafoki ne ya kai kudirin dokar majalisar wanda kuma sauran ‘yan majalisar suka amince dashi.