Monday, March 24
Shadow

Labari Me Dadi: Majalisar Tarayya tace hukumar sadarwa ta NCC ta gaggauta toshe duk wani shafin dake nuna bidiyo da hotuna na tsìraìcì watau Blù Fìm

Majalisar tarayya ta amince da kudirin dokar toshe duk wani shafin yanar gizo dake nuna Bidiyo da hotunan tsiraici wanda aka fi sani da Blù fìm.

Majalisar tace hukumar sadarwa ta kasa,NCC ta baiwa duka kamfanonin dake samar da Internet a Najeriya umarnin toshe shafukan dake nuna batsa nan take.

Dan majalisa daga jihar Katsina, Dalhatu Tafoki ne ya kai kudirin dokar majalisar wanda kuma sauran ‘yan majalisar suka amince dashi.

Karanta Wannan  Matashiyar jarumar fina-finan Hausa, Radeeya Jibril ta yi aure inda tace ta yi bankwana da Fim

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *