
Karamar Ministar Ilimi, Suwaiba Ahmad ta jawo hankalin Gwamnonin Arewa da cewa, su sake tunani kan kulle makarantu da suka yi saboda zuwan Azumin watan Ramadana.
Tace musulunci bai farlanta kulle makarantu ba a yayin azumin watan Ramadan.
Ta bayyana hakane a yayin wata hira da aka yi da ita a gidan talabijin na ChannelsTV.
Jihohin Kebbi, Bauchi, Katsina da Kano ne suka kulle Makarantu saboda zuwan Azumin watan Ramadana inda suka ce sun bayar da wannan hutu ne dan baiwa dalibai damar Azumtar watan da yin Ibada yanda ya kamata saidai hakan ya jawo cece-kuce.
A ci gaba da jawabinta, Minista Suwaiba ta bayyana cewa, A zamanin Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) har yaki yaje a cikin watan Ramadana dan haka Azumi bai hana mutum gudanar da ayyukansa na yau da kullun.
Ta bayar da misalin cewa koda a kasashen da musulmai suka fi yawa irin su Saudiyya da sauransu basa bayar da hutu saboda watan Ramadana.
Tace hakkin gudanar da makarantun Firamare da sakandare yana karkashin ikon jihohi ne dan haka su nasu shawara ne da jawo hankali, inda tace yanzu haka suna kan tattaunawa da jihohin dan su janye wannan matsaya tasu.