
Sanata Natasha Akpoti da majalisar dattijai ta dakatar saboda zargin karya dokar majalisar ga dukkan alamu bata hakura ba.
A wani taron mata ‘yan majalisa na Duniya da aka yi a majalisar Dinkin Duniya dake birnin New York na kasar Amurka, Sanata Natasha Akpoti a can ma ta taso da maganar dakatar da ita.
Tace an mata rashin adalci da take hakkinta, inda tace akwai yiyuwar ma a tsareta a birnin New York.
Ta bayyana cewa, tana fargabar tana cikin matsalar tsaro.