
Kwana daya bayan da tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bar Jam’iyyar APC zuwa SDP, wani Bidiyo ya bayyana inda aka hango Sanata Godswill Akpabio da Sanata Barau Jibril suna ganawa da shuwagabannin Jam’iyyar.
Saidai hutudole bai iya tantance bidiyon sabone ko tsoho ne ba.
Saidai ko da bidiyon tsoho ne hakan na alamta cewa akwai yiyuwar wata kullalliyar Alaka tsakanin Jam’iyyar APC da SDP.
Dama dai tuni wasu ke dari-darin akwai yiyuwar an saka munafukai cikin Jam’iyyar SDP daga bangaren gwamnati dan su lalata tafiyar ‘yan Adawa.