Saturday, March 15
Shadow

Da Duminsa: Kwanaki 2 kacal bayan komawar El-Rufai SDP, Rikicin cikin gida ya kunno kai a Jam’iyyar

Rahotanni sun bayyana cewa kwanaki biyu kacal da komawar tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai Jam’iyyar SDP, rikcin cikin gida ya kunno kai a cikin Jam’iyyar.

Rahoton yace Sakataren Jam’iyyar, Olu Agunloye ne ya nemi daukin shugaban ‘yansandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun inda yace ana shirin tsigeshi da karfin tsiya daga kan kujerarsa.

Rahoton yace wasu ‘yan Jam’iyyar dake goyon bayan tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad da ya koma Jam’iyyar ne ke neman tsige Olu Agunloye daga mukaminsa.

Sakataren ya kuma bayyana cewa, wanine yayi amfani da takardar karya yake masa barazanar saukeshi daga kujerar sa.

Dama dai tuni rade-radi ya fara yaduwa inda ake zargin cewa, Jam’iyya me mulki, APC ko Gwamnatin Tinubu ta dasa munafukai a cikin Jam’iyyar.

Karanta Wannan  Hukumar 'yansandan Najeriya zata hukunta 'yansanda masu cin zalin Direbobi suna karbar musu kudi a jihohin Inyamurai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *