Monday, May 19
Shadow

Bani da tabbacin tsaron rayuwata, za’a iya kamani a tsare ba da son raina ba>>Sanata Natasha Akpoti ta koka

Sanata Natasha Akpoti ta koka da cewa, tana cikin fargabar tsaro.

Sanata Natasha ta bayyana bakane a majalisar dinkin Duniya inda aka yi zama na mata ‘yan majalisa a Birnin New York City na kasar Amurka.

Bayan data gabatar da korafi kan dakatar da ita da aka yi daga ayyukan majalisar Najeriya, Sanata Natasha Akpoti tace tana fargaba kan tsaron kanta.

Tace za’a iya kamata a tsare ba bisa son ranta ba a birnin New York City na kasar Amurka inda tace kuma tana zargin Gwamnatin Najeriya da hannu game da hakan.

Karanta Wannan  Watanni 7 bayan da Kotun koli tace a rika baiwa kananan hukumomi kudadensu kai tsaye ba tare da sun bi ta hannun gwamnoni ba har yanzu ba'a aiwatar da hukuncin ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *