
Wani bincike da aka gudanar ya nunar da cewa ana samun kudi sosai a Najeriya amma mafi yawancin ‘yan kasar basa shaida hakan.
Rahotan wanda kamfanin dillancin Labaran Najeriya, NAN ya ruwaito yace duk da kudin da Najeriya ke samu amma mafi yawancin ‘yan kasar watau kaso 63 cikin 100 na fama da matsanancin Talauci.
Rahoton yace mafi yawanci matane suka fi fuskantar matsalar Talauci inda kuma basa samun ilimi yanda ya kamata.