
Majalisar Dattijai ta mayarwa da taron mata ‘yan majalisa na Duniya dake gudana a majalisar Dinkin Duniya dake New York City na kasar Amurka martani kan dakatar da sanata Natasha Akpoti.
Sanata Natasha Akpoti da majalisar dattijai ta dakatar ta halarci taron inda ta gabatar da korafin dakatar da ita da aka yi, duk da majalisar tace mata ba abinda ya tarasu a wajan kenan ba amma ta sha alwashin ji daga bakin majalisar dattijai ta Najeriya kamin daukar mataki.
A martanin majalisar dattijai ta Najeriya wanda shugaban majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele ya aikewa majalisar Dinkin Duniya kuma ‘yar majalisar wakilai dake halartar taron, wadda kuma itace shugabar kwamitin kula da harkokin mata da jin dadi na majalisar watau, Honorable Kafilat Ogbara ta karanto ta kishi cewa.
Muna sanar daku cewa, ba’a dakatar da sanata Natasha Akpoti ba saboda zargin neman lalata da tawa kakakin majalisar dattijai ba, an dakatar da itane saboda rashin da’a da rashin bin dokokin majalisar.
Majalisar tace tana karyata duk wata kafa dake yada labaran karya gane da dakatar da sanata Natasha Akpoti, sun dakatar da itane saboda rashin bin dokokin majalisar.
Kafilat Ogbara, bayan ta kammala karanto wannan takarda ta bayyana goyon bayan ta na ganin an yi bincike kan zargin da sanata Natasha Akpoti kewa kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio.
Sanata Natasha Akpoti kamin dakatar da ita, sau biyu tana kin tashi tsaye a yayin da kakakin majalisar Godswill Akpabio ke shiga majalisar kamar yanda dokar majalisar ta tanada, kuma an gargadeta kan hakan amma bata daina ba.
Hakanan Sanata Natasha Akpoti ta ki bayyana a gaban kwamitin da’a na majalisar dake son bincikenta.