Monday, March 24
Shadow

Sai da Buhari ya amince sannan na bar APC zuwa SD, Saboda babu wani abun da nake yi ba tare da na sanar da shi ba>>El-Rufai

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce bai bar jam’iyya mai mulki ta APC ba har sai da tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya amince da batun barinsa jam’iyyar APC da komawa jam’iyyar SDP.

“Da saninsa na bar APC. Sai da na je ranar Juma’a na faɗa masa cewa zan bar jam’iyyar. Saboda babu wani abun da nake yi ba tare da na sanar da shi ba.

Ko lokacin da nake gwamnan Kaduna da zan naɗa kwamishoni sai da na kai masa jerin sunayen domin ya duba ya gani ko a ciki akwai wanda ya taɓa zagin sa.

Bayan ya duba ya ce ba matsala Allah ya yi albarka. Duk abin da zan yi sai na yi shawara da shi.” In ji Malam El-Rufai.

Karanta Wannan  Ji abinda Bello Turji yayi bayan da yaga sojoji sun kashe me gidansa

Ko El-Rufa’i na da ubangida na siyasa?

Da BBC ta tambayi Malam Nasiru El-Rufai ko yana da ubagida a siyasa? Sai ya ce ba shi da shi amma kuma yana da waɗanda yake neman shawarwarinsu a siyasance.

“Mene ne ubangida. Ina da masu gida da nake shawara da su waɗanda duk wani abun da zan yi sai na faɗa musu kuma idan bayan sun saurare ni suka nemi na dakatar da ƙudirina ina dakatarwa.

Ubangidana na farko shi ne Muhamamdu Buhari. Sauran kuma ba zan faɗa ba saboda idan na faɗa za a matsa musu.” In ji Nasiru El Rufa’i.

Ko El Rufa’i ya yi da-na-sanin goyon bayan Tinubu?

Malam Nasiru El-Rufai ya ce duk da Tinubu bai yi masa abin da yake so ba amma ba ya da-na-sanin goyon bayansa.

Karanta Wannan  Najeriya ta ware biliyan 60 na ciyar da ƴan firamare a 2025

“To ban yi da-na-sanin goyon bayansa ba amma ina jin kamar an yi min bazata. Dalilin da ya sa ba na da-na-sanin goyon bayan Tinubu saboda dalilai guda biyu.”

“Na farko, shugabannin Yarabawa daga kudu maso yammacin Najeriya sun zo Kaduna suka same ni da batun cewa Musulman ɓangarensu na fuskantar ƙalubalen siyasa. Wannan ne dalilin farko da ya sa na goyi bayan Tinubu.”

“Sai dalili na biyu na goyon bayan Tinubu shi ne saboda mun amince cewa 2023 kujerar shugabancin Najeriya ya kamata ta koma kudancin Najeriya domin a samar da daidato da adalci a ƙasa.” In ji El Rufa’i.

Me ya sa El-Rufa’i ya bar APC?

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya shaida wa BBC cewa ya bar jam’iyyar APC ne bayan gano cewa jam’iyyar ta sauka daga turbar da suka ɗora ta.

Karanta Wannan  Me magana da yawun shugaban kasa ya nemi a zartar da hukuncin ķķìsà kan matashiya 'yar bautar kasa data soki Gwammatin Tinubu

“Jam’iyyar APC ta bar abubuwan da suka sa aka kafa ta. Ta bar al’umma. Kowa yana aikin kansa. Kowa yana neman kuɗi. Gwamnati ta zama gwamnatin kasuwanci. Ta zama gwamnatin komai yana da kuɗinsa.

Kuma babu adalci. Ba a san wanda ya yi wa jam’iyya aiki ba ballanta a saka amsa.- Kowane muƙami za a yi sai an je an ɗauko yaran Legas. To jam’iyyar ta mutu. Wannan ya sa na tuntubi Tunde Bakare da Buhari da Abdullahi Adamu da Adams Oshiomhole da kuma Bisi Akande” In ji El-Rufa’i.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *