Saturday, March 15
Shadow

Gwamnatin Buhari ce mafi muni a Tarihin Najeriya amma naga Alamar Gwamnatin Tinubu na neman yin abinda yafi muni>>Tsohon Shugaban kasa, Obasanjo

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[“local”],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana Gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da cewa, itace gwamnati mafi muni a tarihin Najeriya.

Ya bayyana hakane a cikin wani sabon littafinsa da ya rubuta me suna “Nigeria: Past and Future.” inda yace amma yaga Gwamnatin Tinubu ta kama hanyar zarce ta Buhari wajan zama mafi muni.

Obasanjo ya rubuta littafinne a yayin da ya cika shekaru 88 da haihuwa.

Ya bayyana aikin gina titin Lagos zuwa Calabar da ake kashe Tiriliyan 15.6 wajan ginashi a matsayin bata kudi da cin hanci da rashawa inda yace duk da sukar aikin da zanga-zanga da aka yi dan jawo hankalin gwamnati kan canja matsayinta akan gina titin amma ta yi kunnen uwar shegu.

Karanta Wannan  Wata mata me suna Salamatu ta kkàshe Mijinta a jihar Bauchi ta hanyar daba masa wuka

Hakanan ya bayyana gina gidan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima akan naira Biliyan N21bn a matsayin barnar kudi.

Saidai kokarin jin ta bakin Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari yaci tura inda aka tuntubi kakakinsa, Malam Garba Shehu amma babu wata amsa.

Hakanan an yi kokarin jin ta bakin Tsohon ministan harkokin shari’a kuma babban lauyan gwamnati a zamanin Mulkin Buhari, watau Abubakar Malami shima dai yace a bashi lokaci ya karanta littafin ya ga ainahin abinda Obasanjo yace kamin ya bayyana ra’ayinsa.

Saidai fadar shugaban kasa ta bakin daya daga cikin masu baiwa shugaban kasar shawara kan sadarwa, Sunday Dare ta bayyana cewa, aikin gina titin Legas zuwa Calabar babban aiki ne da zai kawowa mutane ci gaba.

Karanta Wannan  Allah Ya Yiwa Alhaji Ali Obobo Da Ya Taba Zuwa Ƙasar Saudiyya Kan Keke Rásųwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *