
Wata mata a jihar Legas tasa ‘yansanda sun kama mijinta aun kulle bayan da ya kara aure.
Mutumin me suna Charles Chiawa an tsareshi a ofishin ‘yansanda kamar yanda matarsa, Uche Chiawa ta bukata.
Sun shafe shekaru 20 da yin aure inda Charles yace sun fara samun matsala ne bayan da ya kara aure har ya haihu da amaryarsa.
Yace yana da damar kara aure saboda auren gargajiya aka musu shi da uwar gidansa.
Saidai matar tasa Uche tace ba auren gargajiya kadai suka yi ba, hadda na kotu kuma tace yana yawan dukanta ne shiyasa tasa a tsareshi.
Rahoton yace uwargidan mutumin na da alaka da wata DPO na ‘yansanda wanda hakanne ya bata damar sawa a daureshi.
Amaryarsa ta je ofishin ‘yansandan inda ta nemi a sakeshi amma aka ki bata belinsa aka koreta.
Saidai da aka nemi jin ta bakin ‘yansandan sun ce ba zasu bayar da labari a waya ba saidai a ke ofishinsu inda da aka gaya musu zuwan ba zai yiyu ba sai suka kashe waya.