Friday, March 28
Shadow

Bamu san da zaben kiranye da akewa Sanata Natasha Akpoti ba>>Inji INEC

Hukumar zabe me zaman kanta, INEC wadda itace ke da alhakin gudanar da zaben yin kiranye na duk wani zababben dan siyasa tace bata san da maganar zaben kiranye da akewa Sanata Natasha Akpoti ba.

A jiyane dai Bidiyo da hotuna suka bayyana inda aka ga mutane da yawa a mazabar sanata Natasha Akpoti suna gudanar da abinda aka kira da zaben kiranye dan ta dawo gida ta daina wakiltarsu a majalisar Dattijai.

An gudanar da zaben yanke kauna ga Sanata Natasha Akpoti a karamar hukumar Okehi dake jihar.

Wani me suna Nura Abdullahi da aka yi hira dashi game da lamarin yace suna zabenne dan Sanata Natasha Akpoti bata wakiltarsu da kyau sannan kuma ta kasa magance matsalolin talauci, Ilimi da gyaran abubuwan more rayuwa.

Karanta Wannan  Hoto: Davido ya nuna yanda yayi zabe a kasar Amurka, Saidai 'yan kasar Africa ta kudu sunce karya yake a bola ya dauki kuri'ar yayi hoto da ita dan ace shi dan America ne

Saidai an gano cewa an yaudari mutanene da cewa za’a basu tallafine amma da suka je wajen aka ce musu zabe za’a yi dan yiwa sanata Natasha Akpoti kiranye.

Shima dai kwamishinan zabe na jihar, Gabriel Longpet da aka tuntubeshi game da lamarin yace bai san da maganar yiwa kowane dan siyasa kiranye ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *