Sunday, May 18
Shadow

Nine kadai zan iya kawowa kasarnan ci gaba, Hadakar Atiku, El-Rufai, Rotimi Amaechi, da Peter Obi taron mutanene wanda ke son kansu kawai ba son Al’umma ba>>Inji Tinubu

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana hadakar da manyan ‘yan Adawa suka yi da taron wanda damuwa tawa yawa.

Ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Bayo Onanuga.

Hakan na zuwane bayan da Atiku Abubakar, Nasiru Ahmad El-Rufai, Rotimi Amaechi, Peter Obi, Kayode Fayemi da sauransu suka hada kai suka ce zasu kayar da Tinubun a zaben shekarar 2027.

Sanarwar ta fadar shugaban kasa ta bayyana hadakar ‘yan Adawar da cewa masu son kansu ne kawai ba masu kishin al’umma ba.

Ya kuma bayyana cewa ci gaban kasa ne Bola Ahmad Tinubu ya saka a gaba, kuma shi kadai ne zai iya kawo ci gaban dan haka ba zai bari wasu taron sakarkaru su dauke masa hankali game da aikin da yake ba.

Karanta Wannan  Ban san ta yaya suke iya bacci ba yayin da 'yan tà'àddà ke kàshè mutane>>Atiku ya koka kan matsalar tsaro, yace shuwagabannin da suka zo bayan mulkinsu shi da Obasanjo ne suka kawo matsalar tsaro

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *