Saturday, December 13
Shadow

A yanzu Kotu ta amince a yiwa Sanata Natasha Akpoti kiranye

Babbar Kotun tarayya dake Lokoja ta amince a shiryawa sanata Natasha Akpoti kiranye.

Kotun tace mutanen mazabar Sanata Natasha Akpoti suna da ‘yancin yi mata kiranye kamar yanda kundin tsarin mulki ya basu dama.

Kotun tace mutanen mazabar zasu iya ci gaba da gudanar da zaben kiranyen da suke shiryawa Sanata Natasha Akpoti amma su bi doka da oda wajan yin hakan.

Kotun ta bayyana hakane bayan da a ranar Alhamis tace a dakata da maganar yiwa Sanata Natasha Akpoti kiranye.

Karanta Wannan  Laftanar Buba Hamza Kènan Da Aka Ķàšhè A Fagen Dàga A Jihar Borno Bayan Kwanaki Kadan Da Kara Masa Girma A Gidan Sojà

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *