Wednesday, April 30
Shadow

Za’a biya matasa da suka kammala Bautar Kasa karin kudin Naira 77,000>>Inji Hukumar NYSC

Shugaban hukumar NYSC ta bautar kasa, Brigadier General Olakunle Nafiu ya bayar da tabbacin cewa, matasan da suka kammala bautar kasa na karshe zasu samu karin Alawus din da aka yi na Naira 77,000.

Ya bayyana hakane ranar Alhamis a Abuja wajan wani taron wayarwa da juna kai.

Sai a watan da ya gabata ne dai aka fara biyan matasan masu bautar kasa karin kudin 77,000 duk da cewa tun watanni 8 da suka gabata, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sanyawa dokar karin mafi karancin Albashi hannu.

Ya bayyana cewa zasu biya matasan da suka gama kwanannan bashin da suke bi na karin 77,000 da aka yi.

Karanta Wannan  An gargadi gaba dayan mutane miliyan 10 dake zaune a birnin Los Angeles su shirya ficewa daga garin saboda Wata guguwa na shirin hura gobarar dake kan ci ta mamaye duka garin

Yace da zarar sun samu kudin, zasu biya matasan dan suna da bayanansu na banki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *