Mataimakin Peter Obi a takarar shugabancin Najeriya da suka yi a shekarar 2023, Datti Baba Ahmad ya bayyana cewa ba zai daina fada ba cewa, Peter Obi ne ya lashe zaben shekarar 2023.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV.
Yace a lokacin da ake aikawa da sakamakon zabe ga hukumar INEC an kulle dadamalin yanar gizo da ake aikewa da sakon.
Yace aka koma karbar sakon da hannu inda aka juya lamura. Ya kuma kara da cewa jam’iyyarsu a yanzu ta fi jam’iyyar CPC a zaben 2013/2014 karfi nesa ba kusa ba.
Ya kara da cewa, tattalin arzikin Najeriya sai kara durkushewa yake, sannan kuma akwai cin hanci da rashawa sosai.