
Tun bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya tafi kasar Faransa a ranar 2 ga watan Afrilu, fadar shugaban kasar ta fitar da sanarwar cewa zai yi sati biyu ne.
Saidai yayin da ake tsammanin zai dawo ranar 16 ga watan Afrilu, shugaban kasar bai dawo ba inda musamman ‘yan Adawa suka fara tambayar ba’asi.
Fadar shugaban kasar ta sake fitar da sanarwa inda tace shugaban kasar yana nan lafiya kuma yana gudanar da aiki daga can kasar Faransar da yake.
Saidai hakan a cewar masana ya sabawa aiki inda bai kamata ace daga kasar Wajene shugaban kasar zai rika gudanar da gwamnati ba.
Abubuwan da dama sun faru musamman bangaren matsalar tsaro inda aka yi kashe-kashe amma shugaban kasar bayanan inda daga can kasar Faransa ne ya baiwa jami’an tsaro umarnin cewa su magance matsalar da kakkausar murya.
Fadar shugaban kasar dai ta bayar da tabbacin shugaban kasar zai dawo amma bata saka rana ba.
Lamarin yasa mutane na ta yin tambayoyi kala-kala.
Inda wasu ke zargin akwai wani abu da ake boyewa ‘yan Najeriya.