
Marigayi shugaban cocin katolika da ya mutu, watau Fafaroma Francis ya bar wasiyyar cewa, kada a saka masa kayan Alatu a kabarinsa.
Tun a shekarar 2022 ne ya rubuta wannan wasiyyar inda yace kuma yana so a binneshine a Rome wanda rabon da a binne Fafaroma a wannan waje tun shekarar 1669.
Fararoma Francis ya mutu yana da shekaru 88 inda ya sha yabo saboda soyayyar da yake nunawa Talakawa, ‘yan Luwadi, ‘yan Gudun Hijira, Falasdinawa da sauransu.