
Kakakin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, Bayo Onanuga ya kare maganar ware Naira Biliyan 10 dan samar da wuta ta hanyar amfani da hasken rana a fadar shugaban kasa dake Abuja.
A sanarwar da ya fitar, Bayo Ya bayyana cewa ba Gwamnatin Najeriya bace ka dai ta dauki wannan mataki ba, hadda gwamnatin kasar Amurka.
Yace fadar White House ta kasar Amurka ma da wutar Solar watau Hasken Rana take amfani.
Ya bayyana hakanne bayan da sanarwar ware Naira Biliyan 10 dan saka Solar a fadar shugaban kasa ya jawo cece-kuce.