
Dan fafutuka kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore ya bayyana cewa Gwamnatin Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ta kashe ‘yan Najeriya ne inda ita kuma gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta zo ta binnemu.
Sowore ya bayyan hakane a wata ganawa da aka yi dashi a Symfoni yacm soki gwamnatin Najeriya sabosa hanyar data dauka.
Yace kuma abin takaici shine yanda wasu ke goyon bayansu.
Yace irin su El-Rufai basu ne ya kamata ace suna nemarwa talaka hakkinsa ba, yace mayunwata ne, suna samun abinda suke so zasu koma inda suka fito.
Yace duk a gidan yari ya kamata a sakasu a kulle saboda tsaffin ma’aikatan gwamnatin Buhari ne.
Yace amma idan ‘yan Najeriya suka sha wuyar da ba zasu iya jurewa ba, da kansu zasu fito su yi zanga-zangar juyin juya hali.