Ƙungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta ƙasa a Najeriya ta ce an sake kunna babban layin wutar da aka kashe bayan janye yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC suka yi.
Shugaban ƙungiyar National Union of Electricity Employees (NUEE), Adebiyi Adeyeye, ya faɗa wa jaridar Punch cewa sun kunna layin ne bayan janye yajin aikin a safiyar yau.”An janye yajin aiki kuma hakan yana nufin layin ya koma aiki yadda ya dace. An kunna shi tuni,” in ji Mista Adeyeye.Sai dai har yanzu akasarin ƙasar na cikin duhu duk da wannan iƙirari da shugaban ya yi.Tun a jiya Litinin kamfanin kula da rarraba lantarki a Najeriya TCN ya ce mambobin ƙungiyar ƙwadago ne suka tilasta wa ma’aikatan lantarkin shiga yajin aikin ta hanyar kashe babban layin.