
Rahotanni daga unguwar Gwammaja da ke nan Kano sun bayyana yadda a ka harbi wani rikakken dan daba, Halifa Baba, yayin arangama tsakanin jami’an tsaro da bata-gari a yankin.
A na zargin cewa duk wani kwace da fashi da aikata sauran miyagun ayyuka da sa hannun Halifa Baba a ciki.
Majiyarmu tace bisa dukkan alamu Halifa Baba rai ya yi halinsa.
Shaidu sun ce jami’an ‘yan sandan Dala Division ne su ka dauke Halifa Baba domin ci gaba da bincike.