Kungiyar kwadago ta NLC ta dauko daga matsayinta na sai gwamnati ta biyata dubu dari hudu da casa’in da hudu(494,000) a matsayin mafi karancin Albashi.
A yanzu kungiyar tace zata iya amincewa da dubu dari(100,000) a matsayin mafi karancin Albashi idan gwamnati zata iya biyan hakan.
Hakan ya bayyana ne daga bakin wasu ‘yan kungiyar wanda basuso a bayyana sunayensu ba.
A zama na karshe dai da gwamnati ta yi da ‘yan kwadagon ta ce zata biya Naira dubu sittin a matsayin mafi karancin albashi saidai kungiyar kwadagon tace bata amince ba.
Labari na karshe dai shine wanda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya baiwa ministan kudi, Wale Edun umarnin ya gabatar masa da sabin daftari na biyan ma’aikatan mafi karancin Albashi.