Friday, December 5
Shadow

Ni zan shiga gaba in jagoranci sojojina mu je mu yi rugu-rugu da Iran idan bata bamu hadin kai wajan tattaunawar hanata mallakar makamin kare dangi ba>>Inji Shugaban Amurka, Donald Trump

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya ce da kansa zai jagoranci yaki da Iran idan tattaunawar da ake yi da kasar bai cimma matsaya ba na kokarin hanata mallakar makamashin kare dangi ba.

Yace ba zasu bari Iran ta mallaki makamin ba. Inda ya zargi tsohon shugaban kasar, Joe Biden da barin Iran ta samu tarin arziki.

Da aka tambayeshi ko Shugaban kasar Israela, Benjamin Netanyahu zai iya sawa ya shiga yaki da Iran ba tare da ya shirya ba?

Trump yace a’a, yace yafi son a samu matsaya maimakon yaki amma idan ba’a cimma matsaya ba zai yi yaki da Iran.

Karanta Wannan  A cikin mu,Sanatoci akwai 'yan kwàyà da masu taimakawa masu safarar kwàyà, idan kuma kun yi gaddama, muje kowa a mai gwajin kwàyà ko kuma mu rantse da Qur'ani bama harkar kwàyà>>Sanata Kawu Sumaila ya kalubalanci Abokan aikinsa Sanatoci

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *