Friday, December 5
Shadow

Muma dai Muna goyon bayan a baiwa ‘yan Najeriya damar rike Bìndìgà dan su kare kansu tunda dai jami’an tsaro sun gaza>>Sowore da Solomon Dalung

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung da Dan takarar shugaban kasa kuma mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore sun nemi a baiwa ‘yan Najeriya damar rike Bindiga dan su kare kansu.

Sunce idan aka yi hakan za’a daina kashe-kashen da ake yi a jihohin Benue da Filato da sauransu.

Sun bayyana hakanne a wata ganawa da suka yi da manema labarai a Abuja.

Hakan na zuwane watanni 5 bayan da Sanata Ned Nwoko ya kai kudirin neman a baiwa mutane damar rike makamai dan kare kansu.

Shima lauya dan fafutuka, Deji Adeyanju yace idan dai jami’an tsaro ba zasu iya ba, ya kamata a baiwa mutane damar sayen bindiga dan kare kansu.

Karanta Wannan  Ɗalibai 379,997 za su sake zana UTME ta bana bayan da JAMB ta tabbatar da an samu tangarɗar na'ura

Sowore yace mutane sun daina yadda da kariyar da jami’an tsaro ke ikirrin basu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *