Saturday, December 13
Shadow

Tinubu be yi abinda za’a sake zabensa ba, Masu zagina dan na kaiwa Buhari ziyara bakaken Munafukaine>>Atiku Abubakar

Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bata cika Alkawuran data daukarwa ‘yan Najeriya ba.

Yace dan haka bata cancanci a sake zabenta ba.

Ya bayyana hakane bayan komawar wasu ‘yan PDP jam’iyyar APC inda yace ko a jikinsa.

Hakanan Atiku yace masu sukarsa game da ziyara da ya kaiwa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari munafukaine.

Yace Buhari tsohon shugaban kasa ne kuma me ruwa da tsaki a siyasar Najeriya.

Yace a lokacin da ya rika kaiwa Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ba’a rika zaginsa ba sai da ya ziyarci Buhari.

Karanta Wannan  Duk da Hukumar Hisbah ta Kano tace ta je gidan yarin Goron Dutse ta ga ba gaskiya a zargin Luwadi da ake da yara, Saidai da yawa sun ce basu yadda da binciken na Hisbah ba, ciki kuwa hadda tsohon hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *