Friday, December 12
Shadow

Sarakunan Inyamurai sun ce Tinubu ne zabinsu a 2027

Sarakunan yankin Inyamurai sun yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu alkawarin samar masa akalla kaso 70 cikin 100 na kuri’un da za’a kada a yankunansu.

Sarakunan wanda basaraken Abia, Eze Nnamdi yake jagoranta sun bayyana hakane yayin da suka kaiwa mataimakin kakakin majalisar dattijai, Benjamin Kalu ziyara a gidansa dake Abia

Sunce babban dalilin ziyararsu shine dan mika godiya ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bisa kafa ma’aikatar raya yankinsu.

Sannan sun kuma Godewa Sanata Kalu saboda kokarin da yayi na kafa wannan ma’aikata.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Shugaban Amurka, Donald Trump yace zai hana duk kasashe Matalauta irin su Najeriya, Ghana, Nijar da sauransu zuwa Amirka ci rani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *